Showing 333001 words to 336000 words out of 395027 words

Chapter 112 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx

murhu wayana kuma ya shiga kara a lokacin.

Haka yasa ban karasa fitowa daga dakin ba na juya na dauka Ruth ce take kirana nasan bataga nashigo school bane ranan yasa ta nemeni a waya taji.

Ruth a yanzu itace muke dan sama sama da ita dama munayi amma yanzu shakuwar mu yafi nada sosai da ita don haka ba mamaki idan takira din a yanzu nan na zauna muna hira nake fada mata ai ina arewa nazo wajen iyayyena weekend iya abinda na fada mata ke nan lokacin.

Ina kashe wayan naji muryan yaya murja wace ta shigo da waka sai kuma ta dakata tana fadin me muka samu a gidan haka kamar ana wani shagali sai kamshi duk unguwa keyi har ona Allah ya isa dana shaka ashe a gidan mi kamshin yake tashi kuma ?

Me aka samu hakane ta fada tana duban mahaifiyarta dake can zaune nesa da inda suke aikin cikin kashe murya naji uwar na fadin mairoce tazo ?

Mairo wanan rigidin kuma waya saya badai baba ba don zuwan mairo tana fada cikin gadara uwar tace wani baba ina yaga kudin sayen wanan abu haka ?

Kiyi magana kina fada min abu a dunkule haka waya saye wanan nace mai abu suka sai abinsu ko mekike son ji kuma a,a su kuda ai dole naganki a zaune kato kato ana hade miyau haka ?

Anga ,,,, Sannu da dawowa yaya na fada a bayan ta daga kofan inna ina fitowa ta juyo mukai arba da ita wai mairoce da gaske haka ta fada ?

Na karaso gareta na rugumeta wai dama kin zone da gaske Allah na dauka wasa suke min yaushe kika zo ba labari nidai na danna naga wata arniyar mota wajen gidan nan tana sheki na zata wasu suka ajeta a nan don sauda yawa mutane na paxker motarsu nan.

Nice yaya mun sameku lafiya tace kalau irin na yan duniya din nan mairo kece kika koma haka dama kamar wata hjy can dake ?

Ni mamaki da aljabi duk ya kashe min zuciya wai yaya murjace takoma haka sai wani tsami nake jin yana tashi jikinta amma haka na daure na rugumeta ban saketa ba a lokacin.

Ya murja ai idan naganki wani wajen ba zan ganeki ba kin zama wata hjy dake haka tace to zageni mairo tunda kinga kin fimu a yanzu ?

Haba dai ya murja muyi haka kuma Allah kadai yasan wanda yafi wani har yanzu ashe bakin nan naki yana nan dai ?

Ina zuwa mairo bari na aje kayan infito ta fada kamar wace aka tsikara tayi part dinsu harta kai kofa ta juyo tana fadin mama zo in ganki mana.

Allahuma ajirni fi musibati wa,akkaliflil hairum min,ha abinda yazo min a baki ke nan a daidai lokacin data juya don ta barni a tsaye wajen idan ba karya nayi ba shaye shaye yaya murja takeyi kenan don yanayinta ya nuna hakan a jikinta.

Innalillahi na ambata a fili na samu kujera ina kaiwa zaune a wajen don tashin hankalin da nagani a cikin gidan mi din wanan ba abin tsayawa kushewa banw abin bakin cikine ya samu zuri,an mu hakan.

Jikina yayi sanyi nakurawa waje daya idanu ina tunane daga can inda yy sahura take take cewa dani me kikagani mairo Allah dai ya kyauta kawai ?

Na amsa da Amin jikina duk yayi sanyi a lokacin don ban zaci abin yakai haka gareta ba ai na dauka iya iya shegeb fitsarane kawai take tuntiya dashi a gidan ashe abin ba haka bane ?

Suna shiga lungunsu ta soma fadin mama meyasa baki kirani ba don Allah kinzo kin zauna kamar almajira suna kallonki ?

Murja ina nasan inda kika tafi balle inkiraki koma na kiraki me zakiyi tunda basu shiga gonan mu ba wai yaushe tazone ma take tambayan uwan ?

Jiya da dare sukazo naji kina fadin kinga mota amma ance da jirgi sukazo mana jirgin sama wai haka akace uwar ta bata amsa tana zama wanan fa ta dubi kayan dake zube saman gadon yaya sahura.

Itace tazo dashi tsara na sahurane nan naki gasu can na adana makivta dauki kayan tana dubawa tace shegiya kayan nan zasu kai dubi dari fa mama ?

Dubu dari fa kikace murja Allah mama kayane masu kyau gaske akwai wasu da sukayi ankon zanin nan karamin shi dubu sha tara tara aka basu shi karaminshi sosai makuwa.

Saida tagama duban nata tsab tace bura uba yaya akai haka wai wallahi mama su malam sun cucemu sunci amana mu ba wani ijen da sukaiwa yarinyar nan duk karya sukai muna ashe ?

Kedai bari zancen nan murja ki duba can wai namune abin karyawa mai nemanta ya aiko dashi namu kason ke nan haka dazun da safe aka shigo dashi ga nama tun jiya munci har ya ishemu.

Wanan wani irin mai kudi ta samune wai jifa kafiran motan da aka aje muna kofan gida mama ni ina can labari ya kai min cewa muyi bakin maikudi gidan mu.

Kinji ko har an fara fadan haka wallahi ba karamin cutan mu mutanen nan sukayi ba duk dan abindake gareni ya kare wajen ganin yarinyar nan ta tambade batayi albarka ba sai gashi abin baiko faduwa.

Ato tun farko dai an samu matsala in mairo bata tanbade ba ai mun tambade mu yanzu ko ki duba don Allah yau tsaraban mu ke nan mama inaga na uwarta kuma ?

Kai wallahi sai naci kutumar uban mutanen can da sukai muna karya kan zamuga mugun abu akan yarinyar nan ashe munafukai duk halinsu daya ba gaskiya sukeyi ba yan iska.

Barsu murja don Allah sun riga da sun cucemu yanzu saidai a canza shawara san abinyi kuma inba haka ba mu koma yan kallo a gidan nan.

Yaushe kuma mama nikan kwandalana ba munafukin da zai koma cin kudina da sunan wanan ibilishiyar yarinyar jifa yadda mairo ta koma mama na tsani wanan yar a rayuwana tun tana karamar ta wallahi.

Ai kinga Sahura ta lafe tana lakatan arziki ita kuma wace bata da zuciya sakarai kawai kamar da ita ake hada baki ana karya maganin nan wallahi ni bansan yaushe ta koma haka ba ?

Kamar yadda suke can dakin mama suna kulla nasu nima ina nan zaune imani ya kasheni sai kullawa nake ina kwancewa a raina game da yar uwar tawa dana gani haka yau.

Sabanin nasu shirin nikan mafita nake nema gareta yanzu ba sheri nake kullawa ba a raina din tunane nake yadda zan jawo hankalinta a samu ta gyara halinta.

Daki na tasho na koma don Sallah la,asar bayan na idar najima zaune kafim inna tashigo tana fadin Allah ke nan naga jikin ki yayi sanyi tunda kikaga murja ko ?

Duk da hakan kuwa baisa uwarsu ta gane gaskiya ba ta tuba ta koma ga Allah wajan nan da kika ganta kamar ta kuwata take don bakin ciki ai ladabin shegu tayi na dole badon ta tuba ba don tasan tana tak zamanta yazo karshe ke nan gidan nan.

Amma ina yaya ai tuban mazurune tayi kwanto tayi wajen nan har ta samu lafiya nasan acigaba inda aka tsaya don ba fasawa zatayi ba.

To Allah ya kyauta inna indai har yanzu bata bar mugun abu ba tayi nisa wallahi uwale ce ke kiran inna yasa ta fita nidai naji tana fadin duk maici ya dauka ga abunan Allah ya kawo muna a gida.

Naso inshiga gidan anty fati in samu antyna saidai ban samu time ba don a lokacin makwabtan mu da inna ta aikawa tsarabab da nazo masu dashi suke shigowa gidan tarona tare da godiya.

Kafin wani lokaci labari yabi unguwa cewa na zama wata babba ina nan nazo har hjy Tani saida labarin yakai gareta nan ta samu anty har kofanta tana fadin.

Fati ashe mairo tazone tace wai baki gane matar da take hannunta ba da sukazo wani shekara da ita wanance ai take hannunta din.

Ba,a jima ba na tura uwale takaiwa mommy din sakon tsaraban da nazo mata dashi din kunyace ya kamata sosai a yadda nayi mata din .

Da dare sai gata gidan namu take fadin ai bata san nazo ba saida uwalw taje muka gaisa a cikin mutunci nan inna ke fada mata abinda ya kawoni garin zancen baiko na.

Take tambayan da waye zanyi baiko inna tace jikan gidan malam babbane nan baya ta dai nuna farkn cikinta sosai da jin hakana take fadin mutumiyata ai bata san nazo ba nace zan shiga wajenta kafin in wuce ai.

Da zata tafi inna ta zuba mata nama mai yawa a leda da abin sha ta rakata ta tafi tasan yanzu ba shiri tsakaninsu da mama kamar farko.

Ko gaisuwa daga nan ta tsaya tsakar gida ta mikawa mama din gaisuwan tana fadin Rakiyan malam ina wuni ?

Ta amsa tare da tambayan waye hjy din tace hjy Tanice tace da ita baki shigowa tace sauri nakeyi nazo taron yarintace da zuwa ankai muna tsara dazun shine nazo godiya tare da mata sannu da zuwa.

Kallon yaya murja mama tayi tana fadin kinji ko kinji makircin gado ko wanan yar bata ragawa uwarta komai ba wajen munafunci wai hjy Tani ta aikawa tsaraba don tasan ta zama wani abu yanzu.

Mama ki barsu ni duk latsasu zanyi wallahi ta daiji da yarta da miji ke ganawa azabam gidan aure da wanan bakin aure ai gara babushi yafi.

Tana son fidda yar taki fita tunda ita tayi asirin data kafeta a gidan yanzu ko ance ta fita ai bata iya fita gidan itama.

Kinji mugun abu uwace zatayi asirin da zata kafe ya a gidan miji karshe miji yayi ta kumsa mata bakin ciki kuma bata iya zuwa ko ina duk hiransu yaya sahura na zaune inda ta idar da sallah taba jinsu batace komai ba ga zancen.

Ya Allah kashirya duk dan musulmin da zuciyarshi ta raja,a ga hada wanin Allah da Allah zuciya ta biyewa sabon Allah har mutum ya shagala ya manta da Allah ke yi ba wani ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[10/21, 9:10 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,

🐊9️⃣8️⃣🐊

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

*ZEE MAKAWA NOVELS*

1- TAKARI✈️500

2- FUREN JUJI🌼500

3- TARKO🕸️500

4- BAMU KADAI BANE...🧟‍♀️500

1- SARAUTAR MATA🫅🏻500

2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500

3- BAHAGON RAYUWA 🩸500

4- KANIN AJALI 👨🏻500

5- LOKACIN MUKE⚽ 500

6- MIJIN BUZUWA🐪500

7- SARKA...🪢500

8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500

9- ANA DARA...🐟 500

10- KARAN DAFI...🌾500

11- TUMFAFIYA...🌱 1000

12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000

13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000

14- MURFIN JALLO 🏺1000

15_ HAWAYEN KADA🐊

*Account* No

*ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA*

2254380105 *ZENETH* *BANK*

*PHONE* *NO*

08036959257

Washegari nida yan uwana muka shirya fita zuwa unguwa ina jin uwale na fadin saimu dauki drop ko ya saukemu nace motar dake wajefa da ita zamu fita.

Wazai jamu anty shiru nayi ban bata amsa ba muka gama shiri don har gidan kakannimu nake son muje nace zamu soma da gidansu salma.

Mun fito har kofan mama naje nayi mata sallama akan zamu fita cikin gari zuwa family house dinmu mu gaidasu.

Ta amsa da sai mun dawo muna fita na nufi wajen motan na bude nale fadin ke saudat shiga gaba su kuma su zauna baya.

Uwale ta aje kayan data dauko da zamu tafi dashi can gidan sai kallon mamaki suke min uwalece tace kin iya motane yaya ?

Uwale idan kin karamun maganan baza wurin nan zaki koma cikin gida yanzun nan duk sukai shiru yan sa idon unguwa suka dawo da hankalinsu wajen mu suna bin mu da kallo.

Nayi bissimillah nashiga na zauna nayiwa motar key a hankali nasa ribas muka soma tafiya duk ido yana kan mu na yan unguwa wanan har gobe arewa sai abun mace da ido idan tana driving da kanta .

Wasu motar suke kallo wasu kuma wacece a ciki suke bida ido suna kallo dogon rigace da zata kai dubu hamsin tun lokacin a jikina na dora gyalensa iya kaina.

Munfan gusa kadan uwale ke fada min ga shagon Salis ai haka yasa muna isa naja na tsaya ina mashi horn ga mutane a kofan shigon tsalake da gaban shangon duk sun zuboin idanu ban fito daga motar ba shiya tako zuwa inda muka tsaya yana washe baki da ganina yana fadin hjy mairo jiya nake jin kinzo ai a wajen sahura.

Gaisuwa na mutunci mukayi dashi yana tambayana karatuna nace na kusa kammalawa ai don sauran kamar wata biyu in gama ga baki daya.

Farin ciki ya nuna min karara a fuskanshi yana fadin masha Allah kaga abin Allah ko nayi maki murna sosai mairo Allah yasa a kare a sa,a na amsa da amin ina ciro kudi daga jakata dana riko na baiwa Saudat ta mika mashi.

Ya duboni yana fadin haba dai na meye wanan ba zan karbi kudinki ba mairo karatu fa kikeyi haba dai keko dai son Allah nasan lamarin karatu fa ?

Ai gara ka amsa din bada karatu kadai ta dogara ba can tana aikin ta kwanan nan ma aure zatayi sunzo a tsayar da ranane shine zuwansu.

Wai da gaske don Allah haba dai haba duk wanda ya ganki mairo yaga hutu aje a jikinki don baki kama da wanda ke wahalan karatu ba ni badon naganki dasu ba wallahi ban sheda kece ai ?

Ya mika hannu ya karbi kudin yana godiya lokacin na dauki waya ina magana cikin yaren yarbacin sai kallon mamaki yake min nagama na dago ina fadin to salis sai gani na biyu kuma ke nan ko ?

Mairo nagode kwarai wallahi tunda baki manta dani ba mutuminki ko yana nan yayi hatsari wallahi naji ance ana son fita dashi wajema amma ba halin hakan yanzu kinsan abubuwan yanzu sai a hankali.

Yanzun nan gidansu mukayi mu gaidasu ina aon inga salma sai naga ya kwashe da dariya yana fadin ya kamata ko gaskiya hakan yayi kyau sosai wallahi.

Horn na danyi da motan alaman sallama ya danja baya muka wuce ban tsaya saurarenshi balle ya fadi abinda ba shi ba a wajen.

Da kwatace nakai kofan gidan nasu don unguwar ya kare matsewa saboda sabbin gineginen da akayi cikin unguwa wasu kuma ancanza mai fasali a yanzu don cigaba.

Saida na samu waje na packer saudat ke fadin amma fa ban taba shiga gidan ba gaskiya na dai san a nan suke zaune .

Dubanta nayi ba tare da nayi magana ba Allah da ikonsa wasu yarane suka fito daga cikin gidan ki kira yarancan mu tambayesu ko salma din tana nan ko sin canza gida ?

Ta kira yaran sukazo take tambayansu sukace nan ne gidan zasu wuce ta dakatar dasu su tsaya su tayamu shiga da kayan don har drinks munzo dashi irin na dubiya na fito na gyara muka shiga gaba dayan mu tare da sauran kayan .

Ina jin muryan nam nashi yana tambaya wake da kaya haka kuma yaran da suka rigamu shiga gidan suna fadin bakine sukazo dashi.

Saudatce a gaba sai uwale dasu Abdul ina bayansu mukai sallama muka shiga salma din na zaune kofan kitchen tana gyara wake a cikin tire.

Shi kuma yana saman shimfida ga kafa a daure da a daure ya mike duk kafan yasha dauri irin na asibiti din nan shiya fara fadin wai kamar mairo mana 22 muzanta tana faman dan kame,kame da shigowan bazata din da mukai masu.

Ki kaisu daki mana kin barsu nan waje tsaye ya fada kamar a cikin fada naji tana fadin naga kuna gaisawane ai tunda ba tashi zaka iyayi ka shigo dakin ba.

Wani maganan banzane kuma don ban iya tashi shine ba zaki shiga dasu dakin ba kindai san abinda yasa ba zaki kaisu dakin ba ?

Mai zai hana in kaisu ta fada a muzance ta juyo garemu tana fadin ku shigo daki mairo kunji ?

Don kada tace ko donshi nazo yasa banki ba na juya na bita zuwa dakin saidai nayi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login