Showing 78001 words to 81000 words out of 395027 words
Chapter 27 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
ka koma ko abin sayen goro a karshe kuma yasa maka kahon zukau sai yaga bayansa.
Alh yakubu yana cikin nasu taka mashi burki ga wasu miyagun halin nasa yayi ta bibiyanshi yaga bayanshi Allah bai nufa ba sai wanan katon da dansa yaja mashi yalaucewan nan ya samu dama ga Alh yakubu din.
Saidai hakonshi bai cinma ruwa ba don ko kafiya irin na Alh yakubu ya hana har yanzu burinsa ya cika akanshi .
Kaf abokan hurdansa suyi Allah waddai da hali irin na Alh sanusi na rashin imanin da yake takawa a tsakaninsu na rashin sani balle sabo amma a banza don kamar ma hakan ke karawa arzikinsa habbaka.
Kasa hakkuri Alh yayi ya nufi kasuwan tare da addu,an Allah yasa ya samu Alh sanusi din a shago lokacin yayi sa,a don yana shiga kwanan ya hangonshi a zaune ya sake teba yana shan iskan fanka don sa,an zafine a lokacin.
Yaransa na ganinsa suka taso suna maigaisuwa ta bargirma don zaman mutuncin da akayi a tsakani sama sama ya gaisa dasu ya nufi wajen Alh sanusi din da baida niyar tashi a lokacin don su gaisa kamar yadda sauran abokan hurda suka nuna kulawansu.
Bakin shagon ya tsaya yana fasin mara mutunci mutumin banza wanda ba tunanen Allah ga lissafinsa to naji sakon ka saidai ka sani shi ubangiji mai juya lamarinsane ga bayinsa a duk lokacin da yaso hakan ga bawa .
Dariya Alh sanusi din ya kwashe dashi yana fadin sako yakai maka ke nan da wuri haka aina zata sai an wahala kafin kaji sakona.
Ba wahala ai sako kaba yaron kuma ya fada min saidai ka sani yadda kake sayen kayan bayin Allah a nakashe kaima kulba jima kulba dade sai an sayi naka din a wullakace garin nan.
Haka yadda kake bin matan abokan hurda kana aurewa watarana kaima naka za a aura kamar yadda kaiwa kowa hakan .
To ai Alh yakubu niba laifina bane tayiwa fa aka kawo min donshi yarin yafika matsuwa kuma na amsa da zansaya duk da ina tsoron hali irin naka hada dukiya da mutum irinka tsautsayine don bala,i na iya farwa mutum.
Daka kyautawa kanka idan ka kiyayyi kayana kuwa son haka ahir din ka dako allurana balle wani kaddarana sai Alh sanusi din ya kara kwashewa da dariya yana fadin .
Kaddara kuma ta yaushe ko kana mafalki hakane ai yanzu kuma wanan ya zama tarihi a rayuwanka bakai ba kuwa har yayanka ba wanda zai kara tofowa kuma a gidan ka irin baya saidai labari kuma Alh yakubu.
Tsaya kaji Alh sanusi ni jahilcinka baisa in kaucewa ubangijina har in fadi abinda ban isa ba akaina ko wani bawa nasa don nasan Allah ke bayarwa shi kuma ke karbewa a duk lokacinda yaso.
Don haka nayima kashedi da kayana saika bari bayan raina idan Allah ya karbi rayuwana kana iya kayi abinda ka saba sayen kayan mamaci saika jira kaima kafin azo a sayi naka din wata rana.
Sunyi ba dadi a wajen har abin yayi ta yawo a cikin kasuwan zancen ya koma har kunnen su Alh innuwa a Allah waddai da hali irin na Alh sanusi a ko ina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI KEBBI STATE
[7/18, 8:51 PM] Zainab Idris Makawa Writer: HAWAYEN KADA,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,,,,,,
2️⃣6️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI NAIRA DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZENETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
*ZEE MAKAWA NOVELS*
1- TAKARI✈️500
2- FUREN JUJI🌼500
3- TARKO🕸️500
4- BAMU KADAI BANE...🧟♀️500
1- SARAUTAR MATA🫅🏻500
2- MURICCIN KAN DUTSE...🎋 500
3- BAHAGON RAYUWA 🩸500
4- KANIN AJALI 👨🏻500
5- LOKACIN MUKE⚽ 500
6- MIJIN BUZUWA🐪500
7- SARKA...🪢500
8- ABU CIKIN DUHU⚫ 500
9- ANA DARA...🐟 500
10- KARAN DAFI...🌾500
11- TUMFAFIYA...🌱 1000
12- DUBA MIN BAYA FAKON BIRI..👀 1000
13- JA YA FADO JA YA...🔴 1000
14- MURFIN JALLO 🏺1000
15- HAWAYEN KADA🐊 1000.
_Account No._
_*ZAINAB IDRIS MAKAWA*_
2254380105
ZENETH BANK
PHONE NO.
08036959257
Ranan dai na wuni hira da yan uwana a dakin mune tun bayan da naje har sashen mama na gaida ita tana ta kare min kallon kwam har yakai na gane hakan.
Tunda na dawo ban sake fita ba muna dakin muna hiran mu da yan uwa wani lokacin inna na dan tsoma muna baki a cikon hiran namu.
Baba ya dawo kasuwa da cefanai na kayan miya harda maggi a ciki dasu mai da tantakwashi mai yawa da tsoka ganin haka na fahinci akwai sauki a cikin lamarin baba lokacin don ba kamar yadda na barshi bane a baya.
Naso in fita in taya inna girki amma tayi min ido dana koma na juya da sauri zuwa dakin ashe inna ta fara sakin maganganu cewa wanan dai zuwan bana banza ba kam.
Aiko makaho ya laluba zaigani ace mutum ya koma haka jajiri kamar tsada wai kuma iyayye basu damu ba da sabon sauyin da suka gani ga yarsu sai zancen abin duniya akeyi ana rawan jiki anga banza.
Abinka da uwa hakan yasa inna ta fara faduwan gaba don ita girman da nayi da sauyawa tunda nashigo take mamakin hakan ta manta da cima ba daya ba.
Nikan bansan anayi ba zuwa dare kuma baba na zaune yana cin abinci uwale ke fadin anty mairo tace muci abinci ita ba zataci abinci ba yanzu wanka zatayi ta kwanta.
Ai daiyi mugani ga zance nan yana fita fili ai jn babu wata a kasa ta yaya za ace mutum yayi shekaru a wani waje sai a turoshi gida shi kadai haka zikau babu ko ga kayanku nan mun gode.
Wama ya sani ko anje an hakewa maigida matar gidan ta gane ta izo keya zuwa gida haka kai tsaye a lalace har ma dai ta rasa abin fada a lokacin saboda sheri.
Inna dake gaban baba a lokacin yana sauraren zancen mama din daga shiyanta cikin daga murya take wanan zance don suji inna tace da baba din.
Tun dazun take fadin maganganunta wai ga sauyi nan ta dawo dashi amma rashin hankali da kwadayi ya hana mu kwantar da hankali mugane aiba haka mairo take ba.
Innalillahi wa inna alaihim raji,un wai kuwa wanan karon ba zan saki Rakiya ba da sauri inna tace a,a malam mu fara tantacewa ni tunda ta soma wanan zancen gabana ke faduwa wallahi.
Kema baki yarda da yarki bane kome a,a ba hakana bane indai bataje can ta sauya halinta ba aini duk cikinsu hankalina yafi kwanciya da ita kasani.
Don Allah barmin wanan zancen banzan na Rakiya kishine da bakin ciki da harta kasa boye hakan yasa ta soma haukanta ke baki san halinta bane da zaki biyewa shirmenta.
Mlm kaji abinda ta fada fa yanzu waya sani ko taji wani zancene ta boye muna dama .
Kaiyya amma ko kin ban mamaki mutumin dakewa kadangare da kaji sheri don tayiwa mutum shine zaki zargawa yarki abinda bashi ba ?
Tayi shiru Allah dai ya gyara ba wanda ya koma kan mama din a ranan taci zarinta harta gaji kowa ya shige dakinsa da iyalinsa ya kwanta.
Ni dai tunda nagama shirina bayan nayi wanka na dan tsakuri abinci naci tun lokacin na kwanta barci ban san lokacin da suka gama ba kowa ya kwanta.
Sai cikin dare nake jin ana ja min kafa na bude ido innace akaina da tocila take fadi a hankali ke bude ido muyi magana kinji.
Da sauri na bude idon nawa ta dan kara rage murya tana fasin akwai matsalane tare dake suka barki ke daya kika dawo muna don kinji mamanku ta fara fadan hakan a cikin gori.
Matsala inna tame lafiya lau muka rabu anty din ma dan matsala suka samu din ta tare zamuzo da ita gidan nan amma tana nan tafe tace nan gidan .
To nidai don Allah har yanzu ina tokonku iyami ku rufamin asiri don Allah ku kama mutuncin ku da kimar ku hankalina ya tashi da wanan zance na yaya wallahi.
Nikan ba abindake damuna inna kuma lafiya lau nake dasu nan ta fahinci ban ma gane me take nufin mama na hasashe a kaina ba lokacin tace tashi ki rufe maku kofa.
Tana fadan haka nasan zata gun babane dama haka mukeyi na mike na rufe kofan na jima banyi barci ba ina tunanen halin zaman gidan namu.
Washegari koda natashi nayi sallah ban kwanta ba na dan taya innan mu aikinta na safe sai bayan mun gamane na koma nayi wanka na shirya a cikin wani dogo riga fitted .
Kayan sun matukar karban jikina zakice ba dinkin telolin mu bane na Nageria don dinkin lagos daban yake komai sai an fitar dashi yadda ya dace.
Zama nayi muna karyawa don baba ya aika an sayo min masa kosai da sukari saina debe kokon da mama ta dama ina sha tare da yan uwana.
Yaya hajara tazo kofan mu tana fadin ina bakuwar lagos din na mike na fito waje ina dan murmushi nace yaya ai naje gaidaku na samu kuna barci sai mama na samu a falke muka gaisa.
Karasa fitowa nayi ina magana gaba dayansu ashe suna zaune a tsakar gida sun zubo min idanuwa suna kare min kallo yasa muka gaisa da ita na gaida yaya sahura daga nisa itama.
Na jiya naji tana fadin yaushe zaku koma nace wallahi ban sani ba anty zamu kwana biyu dai a nan sukace daga inda mama take mukaji tace komawa banzane halan ?
Andai dawo ke nan ai angama bariki sun samu sun ingizo muna keyarta gida da abin kunya wanga dabian dame yayi kama mutum na shiga kamar dan wani kafiri dashi haka mu dai ji in gaskiya ya baiyana muna nan muna gani muna kuma saurare da kunnuwan mu.
Rakiya nine kafirin ko ke naga dai mairo yarkice kema duk abinda kike nufi ya samu mairo a can kema ya sameki ai don ko ban raye mairo jininkine kema ?
To wai mama wanan magana dame yai kama na fada maki tun jiya ki bari kinki yarinyar nan bata dawo da wani abin kunya ba kin matsa da irin maganganunki kina jifansu dashi haka haba mama sin Allah dai ?
To uwata kwabe min baki in sani aiban sani ba saikin fada nagani kuma za a hanani magana in fadane don ina tsoron wani ?
Jikinane yayi sanyi kafin naji yaya sahura na fadi itama ina ruwanki inkin gani mama balle me kika gani don Allah baki dai barin wanan halin mama.
Ganin yadda yaran suka hauta da fada yasa baba yai shiru kila saiga inna ta fito daki tana fadin abindake rantane take fada maku ai ku baku fahinceta bane so tayi ai ta dawo da abin kunya Allah bai nufa ba shine babban bakin cikin yaya tun jiya.
To kingani kinkai ga abinda kike son ji mamako tayi cikin inna da bakaken magana a kaina sai fadi takeyi ta dawo mana dashi abin kunya ko bai fito fili ba ai a baiyane yake.
Suna dai rikicinsune mukaji sallama na sheda muryan Antyna ta shigo dauke da yarta a kafadanta nasan don ruwan kwatan data gani a gaban gidan mune yasa ta dauki yarta ta saba.
Cikin murna nake fadin lah anty nayi kanta da murna take fadi da turanci ba dole ki ganni ba baby ta hanamu barci jiya wai sai ankawota wajen ki na karbi yar ina tambayanta meyasata kuka ?
Sai fada ya dakata kallo ya koma garemu din turancin da mukeyi da anty din da yarta har mama tayi tsaye tana kallon mu.
Na juya wajen inna ina fadin antyna ke nan mama ga antyna da nake wajensu ta biyoni tayi yaken dole a fuska tana fadin sai gata kuwa.
Na juya inawa anty din bayanin kowa da dangantakarmu na nuna mata harsu yaya dake zaune sai cewa tayi duk kinfi yan gidanku kyau maryam.
Inna tacewa saudatu ke shiga ku gyara mata waje ta shiga daki ta juya da sauri zuwa dakin namu gaisawa takeyi dasu a cikin hausanta mai surki suka gama muka shiga daki tare dakin innan mu sosai taji dadin yadda aka nuna mata kula da kauna ita da yarta don yan uwana nason su karbi Amira a hannuna amma taki zuwa muna dariya don hausan da suke mata din a lokacin.
Ikon Allah sai kuma ga kwalaye ana shigowa dasu wanda abin ya bawa kowa mamaki sun gaisa harda baba ta shigo dakin mu din ta zauna.
Aka fara gaisuwan mutunci ita da innan mu a lokacin ina jin inna na tambayan har baba badai matsalan komai ko tace baba matsala ga wanan ta nunani tace ko daya wallahi maryam yarinyace mai mutunci data san ya kamata yana da wuya maryam ta batawa mutum rai gaskiya.
Naji dadin yabon da anty tayi min din a gaban iyayyena duk da nasan banda matsala dasu din amma kuma wanan ya kara wankeni garesu ai a yanzu don hankalinsu zai kara kwanciya ga zargin da mama ta jefeni dashi.
Take fadin kayan tea ta sayo muna sai noodles da yan sauran tarkace don tasan Paapa ba zai saya muna ba nayi godiya inawa inna bayani itama godiyan dai tayi mata a lokacin.
Sallaman anty Fati mukaji ta shigo tarona ita da danta rike a hannunta na mike naje na rungumeta muna murna da ganin juna anty dai na zaune tana kallon mu nayiwa anty Fati din bayanin antyna a lokacin ta juya suna magana da ita.
Sai rana nasan anty fati ba karamar wayayya bace ashe don hiran lagos da sukeyi ita mahaifinta dan sandane sunyi yawon gari gari dashi a lokacin.
Kinsan halin mata sai gashi sunyi sabo a dan lokaci har anty din ta sake da ita suna hiransu kamar sun taba haduwa a baya .
Girki na musanman aka hada masu cikin dan lokaci har angama ni ban sani ba ko mama ta fitane don ban kara jin duriyanta ba a gidan.
Gashi har bayan azahar suka kai a gidan mu kafin muka kwasa zuwa gidan anty fati data mike don zuwa gida dolw har dani aka shiga ina gaida hjy wai bata ganeni ba nayi dariya ina fadin mairoce fa hjy .
Cikin mamaki tace mairo kece kika zama haka lalai kin taka lagos da kafan dama mun dade muna gaisawa ina tambayanta bayan rabo ban zata zanga wanan daman a wajenta ba lokacin sai gashi kamar komau bai faru ba a baya tsakanin mu tana min dan haba haba a fuskanta na nuna mata anty tana ta mamaki tana fadin ashe ba tsohuwa nake hannunta ba ?
Tambayan ya ban mamaki nake fadin a,a mama amma zancen Rakiya sai a barshi tace wajen tuwo tuwo aka kaiki sana,an da kukeyi ke nan a can lagos don nace ba gaskiya bane ban komai kawai dai sun rikenine a hannunsu karatu nakeyi kawai a can.
Amma lalai Rakiya dambalaliyar macece mara lissafi mu abinda ta fada muna ke nan ai kina can kina bariki lagos.
Taga bariki dai a cikin kayanta muryan saudatu kanwata ke fadin hakan a bayana na juyo da mamaki ina kallonta tacigaba da fadin sheri dan aikene kaida ja tura zai dawowa ai yanzu dai aiga gaskiya kun gani dan uwan baban mu ya dauketa can take zama da matarshi.
Mun barta nakewa sister dina saudatu fada meyasa ta fadi hakan ga mama tace itama ai abinda take fadi ke nan a kan mu Allah badon su yaya sahura ba da basu fayeyiwa inna rashin mutunci ba niba zan taba ragawa matar nan ba ai itama ta sani tace nafiku bala,i kaf a dakin mu din.
Anty fati ke tambayan me mama ta tsaya fada muna saudat ke mayar mata take fadin makira koma meye tare suka kullashi ai nan ta soma ba anty labarin da ban taba fada mata ba game dani da irin zama da innan mu keyi da mama a gidan mu da nata gidan yadda suke kwasa da hjy Tani a gidan kullum kamar yau aka aurota.
Indai ance mata sun hadu zance dayane akan namiji idan kuma matan aurene to zancen zai dangana da kayan mata a wajen hiran ganin zancen da suka soma yasa nace ina zuwa fita nayi saudatu ta mike tabiyoni.
Nazo fita daga dakin anty fati naji mama na