Showing 291001 words to 294000 words out of 395027 words
Chapter 98 - HAWAYEN KADA BOOK COMPLETE BY ZEEY MAKAWA 2025.docx
hjy takai mata yaron ta gani kuma su gaisa da ita.
Shikan da zai fita tace ya saukesu idan ya tashi bai kiba ya kaisu ba wani saninta sukayi sosai ba dama koda ta shiga saida ta tsaya bayani cewa itace matarshi sanan suka shedata.
Haka sukabi kowa suka gaisa yaro kan an nuna mai kulawa sosai kowa yazo zaice a,a yaron ne nan ya girma haka ai mai wasa da yake yana da kiuya ta koya mai ita kadai ya sani sai bai yarda da kowa a gidan.
Ga zagi da kukan banza zai daga hannu ya zagi babba ko waye wanan halin yayi yaya karima dake zaune ya zagi wata yarsu ta kama hannunshi ta buga a wajen hakan yasa ran uwarshi baci take ta daure fuskanta ga abinda yar uwar mijin tayiwa danta.
Don itafa ba kwabo take bashi kuma bata yarda a tsawata mashi dama nasan a kan wanan halin dole a samu matsala da ita wata rana.
Sun fahinci ranta ya baci da hukuncin da yar uwar mahaifin yaron tayiwa dansu don yadda ta kare daure fuska taki magana da kowa a lokacin .
Hjy din kecewa mu a nan bamu haka yaro yayi ba daidai ba yan uwan ubasa ke tsawata mashi koda uban yana kusa kuwa ki daina hakan tunda bake kadai ke da dan ba.
Cikin kunya da anganota ta soma fadin hjy aiba fushi nayi ba halin yarone dai amma ina kwabonsa da hakan yaki ya bari.
Hjy dai bata tanka mata ba ana azahar tace zata gida hjy din tace ba yace sai dare idan sun dawo daga funtuwa zai biyo ya daukeku ba ?
A,a zan koma inyi girki ta fada tace shike nan idan kun fita sai yara su tsare maki abin hawa a wajen ta bata dubu daya tace tayi kudin mota dashi.
Tun a hanya tasha alwashin ko zata koma gidan nan ba maza ba don yadda kowa ya kama gabashi aka barta a zaune dakin hjy din bai mata dadi ba.
Matsalan da tun farkon zuwanta kano din aka samu ke nan da ita sun fahinci irin mutanen da basu son aiwa diyansu fadane don sai ransu ya baci idan hakan ya faru dasu.
Ina gaban mirrow ina dressing kiranshi ya shigo wayana na daga da sallama ya amsa yana fadin ke dai idan ba an kiraki ba baki kiran mutum kiji lafiyanshi ko ?
Umm,humm mutumin dake gida yana huta da iyali da iyayye wani gulma zai kaini kirashi yace yana jin dadi na katse masa jin dadin rayuwa ?
Hakane kuma amma naga ai ban saka maki dokan hakan ba ko don bukin magaji bai hana na magajiya don ina gida zaisa ba zaki kirani ba ?
Murmushi nayi kina ina yanzu gida na bashi amsa don tun safe kwance nake yanzu nake niyar fita in sayo abu ki jirani nazo na kaiki naji ya fada ya kashe wayan tashi.
Samun kaina nayi da sauya kayan dana saka da farko a jikina na fidda wasu abaya sabo na saka don fitan zai zama kamar outing a garemu tunda yamma ta soma a lokacin.
Ba,afi mintuna arba,in ba tsakani ya iso kofan gidan namu yana horn Amira ta fita ita ta dawo hannunta da kudi tana sheda muna zuwan shi.
Na kara fesa turare a jikina na fito a falo na samu antyna zaune nake fada mata zan dan fita nida Oga tace ya dawo ke nan nace ehh.
Amira tasa kuka wai zata bini kuma ba ai mata wanka ba zata bata min lokaci tunda gashi har ya iso a lokacin.
Ran uwar baiyi dadi da hakan ba na dai fice na barsu na sameshi zaune a mota ya dan kwantar da kanshi alaman gajiya a atare dashi lokacin.
Jin fitowana ya dan dago ya zubo min ido har na karaso infa yake Sallama nayi na tare da fadin sannu da zuwa ki zagaya ki shiga a bude motar take amsan daya ban ke nan a lokacin.
Na zagaya na shiga ya tayar muka bar kofan gidan nama ya soma fadin ina zaki haka kika sha kwaliya ko za ai gasane a garin banda labari kinsan ke member dinsu ce ai ?
Murmushi nayi kafin nace Green land nake son zuwa in duba abu don ba zan iya fadin abinda zan sayo ba din a gabanshi ba.
Okey ya fada ya dauki titi da zai sadamu da can din na kawar da dan shirun da motar tayi da fadin ya kabar su ummah dasu Amira ?
Suna lafiya sunce a gaidake ya fada ummah tace kina da kunya kin fini kunya sosai yadda tajiki a waya kina magana.
Murmushi na danyi kafin nace ai ba a waya ba kadai ina da kunya a gaban na gabana sosai donshi akasan mace dashi dama.
Amma banso ka bata wayan ba ai a lokacin don dana san kana kusa da ita ba zan ma dauki wayan ba gaskiya naji nauyi da kunyan hakan.
Ohh realy na dan rausaya kaina ina lumshe ido tare da jin wani iri a zuciyana yace kiyi hakkuri nayi abinda baki sani ba sam ba zan iya rike zancenki ni kadai a raina ba maryam a yanzu.
Duk wanda yake kusa dani dole ya fahinci irin kaunar da nake maki na fara gabatar dakene a wajen ummah dinne a yanzu don tasan da zamanki a tare dani .
Don idan zance ya taso ba sai na tsaya ina kwanaye kwanaye a kai ba already kowa yasan da zancenmu dama.
Bance komai ba illa jikina dake dan karkarwa naji ya matso kusa dani kadan cikin kashe murya kamar me rada ya soma fadin sai kinyi hakkuri da yanayina ni mutumne dake zuwa ma abu kai tsaye matukar ina ra,ayin abin.
Tsawon lokaci mai dan yawa muna haka motar tayi shiru sai shi dake tukin abinshi naji ya sauke ajiyan zuciya kafin yace wai kinsan mata nawa aka izo min akan na nemesu ayi yar gida a tsakanin mu kuwa ?
Cikin dakiya nace dama haka iyayyen manya suke ai basu yarda dansu yayi zabin kanshi saidai a hada a tsakani don kada dan tallaka ya samu kafa shiga cikinsu mafi yawa a yanzu abinda akeyi ke nan ai a hada aure a tsakani da wata manufa.
Manufar da ba zan taba yarda dashi ba ke nan a kaina a barni in zabi abinda zuciyana yake kauna ba ai min cushen ra,ayin wani ba.
Ni kadai na wahala na nemo abina a yanzu ba zan yarda wani ya kutso a rayuwana yace zai juyani yadda yake so bayan a baya ya kyamaceni sai a yanzune zan zamo abinso a wajensu ?
Wai fa duk mutanen nan maryam da zan fada maki irin rayuwan da nayi a baya dasu zakiyi tir da rashin kunya irin nasu wallahi iam telling you mutanene dake nuna dagani har uwata bamu isa mu,amula dasu ba yan shekarun da suka wuce.
Wanan lokacin ya shude ai suke gani a wajensu na yanzu suke duba a dora sabo ka yarda da zancen iyayyenka don a zauna lafiya da kowa haka nake ganin yafi.
Fuska a daure ya sake juyowa gareni ya kalloni ya juya wani abu naji ya sokeni a kirjina don yadda yanayinsa ya sauya lokaci guda haka.
Karfin hali nayi nace a fili ai gaskiya na fadama daddy kowa a duniyan nan yana son biyayya gana gaba dashi don ya rabu da iyayyensa lafiya .
Kardai kice min kema akwai wanda aka zaba maki dama a matsayin miji can kano dan ban sani ba ina wanan shirmen akanki yanzu ?
Murmushi nayi ina fadin don ka kulani hakan aiba shirme bane don Allah yasan ladan dake cikin hakan da kayi
Beside dai ayanzu dai bani da kowa for now asalima ni yanzu ai karatuna nasa agaba ba tsayawa yin soyayya da wani ba balle a bata min lokacin plan din na ya rushe.
Okey yanzu ni shirme nakeyi ke nan kike nufi da sauri nace No ba abinda nake nufi ke nan ba tambayana kayi nake kokarin fadama a yadda ka sameni.
Nasha wuya daddy ina karama a haka na taso har nazo garin nan hakama mahaifiyar mu har mahaifina nataso nasan irin tsadan wahalan rayuwan da suka shiga sosai a baya akan mu.
Haka yasa nake son nayi amfani da daman da Allah ya ban na zuwana wan,nan garin in tsaya indage inyi karatu ko Allah zai ban wani dama in samu matsayi da zan iya taimakawa rayuwan mu baki daya a gidan mu.
Murmushi naji yayi yana wani tuki a cikin sallo ba tare daya kara ban amsa ba akan zancena wanda nayi mamaki amma nasan don na fada mashi cikin zuciyanane a lokacin.
Cikinshi ya dan buga hakan yasa na juyo na dan kalloshi ya lumshe ido yana fadin sai yanzu na tuna da ko karin safe banyi ba fa.
Why haba dai dolene ciwon ulcer ya kamaka ai ace tun safe amma mutum baici komai ba kuma ba zauna ba zafin nema akace bai kawo samu a rayuwa.
Yanzu me zakaci ke nan a kokarina na ganin wancan maganan da kamar yakewa fushi ya kawu a zuciyanshi don na fahinci mood dinshi ya dan canza a lokacin.
Jin bai ban amsa ba yasa na dan duboshi ashe ya ganni a lokacin yace ban faye son cin abu a waje ba ko yayane abinda aka girkawa mutum a gida yafi safe.
But is too late yanzu ko tafiya daga nan zuwa unguwarku ma aikine a yanzu gara kawai a samu wani abinda ka danci a nan .
Samun halal shine da wuya haka nake tafiya inyi ta wahalan neman irin abincin da nake so na yarda dashi ba komai ne a yanzu mutum zaita durawa cikinsa ba kai baka san dame akayi shi ba ?
Muje hjy hajaru nasan baka rasa wani abinda zakaci a can din inane kuma hjy hajaru yake tambaya nace wani gidan abincine a nan ajagule wasu yan ghana mata ke aiki a wajen.
Okey sai kiyi min kwatance ya fada da kwatancen muka isa wurin dashi tun daga waje yake mamakin wajen .
Muka fito don shiga ciki inda yaga wajen zaka cire takalma daga farko a wani part akwai kuma inda ba sai kacire takalma ba din a saman table zaka zauna kaci abincin wancan kuma a kasa saman dadduma ake ci abincin.
Sannuku da zuwa wata Alh ta juyo guna tana fadin sannu hjy wata bakar dattijuwan mace mai fuska da fara,a take fadan hakan a cikin hausa.
Koda yake ban sani ba ko filubene ku tunda dai na ganku a nan yan gidane hausawa ko fulani me za a kawo maku muna da tuwon gargajiya dawa biski samosa danbu amma gaskiya dambu ya dan dauki awa daya da rabi a kasa akwai waina da miyar taushe akwai kansa akwai na rago akwai kayan ciki insha Allah ?
Ok asamin tuwon dawa naci don Allah ya fada cikin katseta da sauri na daga na dubeshi yace abincina ke nan idan naje Kano gidan malam sai anyi minshi don sunsan ina so sosai.
Matar ta juya sai kuma ta tsaya tana fadin Alh muna da fura ta asali damun hannu da ludayi idan zuma kakeso baka so zuma muna dashi Alh.
Ki hado min da fura amma wanan dashi zan tafi ta juya ta tafi bata jima ba kuwa sai gata da abinci plate biyu ta kawo muna fuska na yamutsa alaman badani ba.
Au bakya cin tuwon ke nan ke a,a please koda muke talkawa gidan mu bamu iya cin tuwon dawa ba gaskiya kona shimkafa ba sosai akeyisa ba sai lokaci lokaci iyakar mu shimkafa da mai da yaji a nan na gwane gaskiya yanzu kuma da ban samu sai tuwon alebo.
Tuwon dawa miyar kuka sai naman tantakwashi da akai amfani dashi ga kamshin man shanu na ainihi yana tashi daga miyar da kamshin dadadawa yana tashi .
Haka ya zauna ya soma ci sosai yana ta ban mamaki duk da hankalina yana gun waya da muke charting da Saudat a lokacin.
Nawa kudin plate ya fada yana dauraye hannunsa a ruwan da aka tanada don hakan jin hakan yasa na dago kai na dan dubeshi kafin na mayar da idona kan plate din naga yaci har wanda aka aje min din yana fadin yes malam yace yafi lafiya a jikin dan adam .
Wanan dn gaskiya bamu saba dashi ba a gidan mu da ace mama nasone nasan da mun iyacin shi don dole sai ya kasance itama bata so aka zauna lafiya.
Yaran yanzu ai baku san me ke baku lafiya ba kinga wanan tuwon a kullum mudu goma mukeyi nasa kafin takwas na dare sai kudi bayama isa idan munyi.
Matar data iso da goran furan da aka hada mashi take fadan hakan garemu ki hado mata ferfesu kayan ciki da na kai a fada muna kudin mu ya fada.
Aiba yawa kudinku idan an hada zai kama dubu goma Alh ta fada hakan yasa hannu a aljihu ya ciro kudin yabawa matar ta tsaya kirgawa kafin ta dago tana fadin kayi kari Alh yace na sani babba na dai kara makine don kon tuna min da gida yau .
Anko gode nagode ta shiga jera mai godiya wanan ce ta kawoni gareku ita zakiwa godiya ta dan juyo gareni tana mika min godiya.
Bamu jima ba ta hado muna muka fito daga wajen mota muka shiga muka bar wajen zuwa green land din wanda ba komai a cikinsa sai kaya irin na kasan waje wanda ba a faye samun irinsu ba sosai ko ina.
Maryam ya fada a kasalance na juyo na dubeshi bai kalloni ba sai tukin da yakeyi yake fadin nagode kwarai da taimakon nan da kikai min a yau.
Don ba karamin dadi naji ba a yau dana dana samu abincin nan kuma nagane wanan waje ina wahala don ban faye son abinci haka irin na zamanin nan na shirmen ba.
Don shi ya n yafi yawa a yanzu ni nafi son local food namu na gargajiya irin haka sai inci in koshi insan naci abinci.
Wanan yasa kikaga ina son mace wace ta iya girki ko wani kalan abincin mu na gargajiya tayi mun ta gargajiya na dinga ci.
Don gaskiya idan na auri macen da bata iya girki ba nasan zan a samu matsala sosai dani a wanan wajen don ni mutumne dan gargajiya .
Kana nufin ita wace ke gida bata iya irin wanan girkin bane tuwone fa kawai ?
Kuma ai ko wace macen bahausa ai zata iya dai mu yaran hausawa idan ba sakaran uwa aka samu wace bata koyawa yarta aiki ba saboda lalaci da gudun abinda ka fada yanzu.
Wanan babban abin kunyane ga mace taje gidan miji ana korafi rashin iya girki ko aiki a kan ta gaskiya.
Balle kai daddy yanzu me zakayi da aure kuma bayan nasan a yanzu baifi da guda ko biyu ba ai a tsakanin ku in ma har ta haihu din ?
Tsaki yaja yana fadin niba wanan zance nake maki ba kuma nataba fada maki ina da aurene wai ?
Nina ban taba fada maki wai ina da aurene ba maryam kuma na tabbata wani ba zai fada maki hakan yayi min sheri a wurinki ba ?
Naji ya fada hankalinshi nakan tukin da yake inda yaci gaba da fadin ba yau ba na fahinci kina kishi akan matana maryam ?
Ni kuma ban taba fada maki cewa ina da mata ba amma kina ta daukan alhakin wace ni kainama ban sanda ita ba ?
Wani irin kunya naji ya lulubeni lokaci guda abinka da tabarman kunya ance da bori ake nadeshi na soma fadin nikan ina nasani tunda namiji haka kamarka ai ba zai zauna haka baida mata ba ?
Allah ko nima shiyasa nake son nayi matar nan da kowa ke min magana yanzu ko zan fara bada doka a gidana yadda naga magidanta nayi ?
Daddy wai da gaske kayi don Allah baka da mata amma kuma naga gidanka tsarin shi irin na mai mata kitchen dinka fa komai na kitchen din mace akwaishi a cikinshi.
To meye mu din dake rayuwa a cikin gidan ba mutane muke ba halan da kikazo ke bakiyi amfani dasu ba ranan ko so kike aje makwabta a aro maki abin amfani tunda kinzo gidan gwauroba.
Dan